Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwallon kafa za ta kara yaukaka zumunta tsakanin Sin da Uruguay
2020-10-23 10:09:25        cri

Yayin da kasar Sin ke kara fadada cudanyar ta da sassan duniya daban daban, wata kwararriya a fannin mu'amalar kasa da kasa 'yar asalin kasar Uruguay Lucia Fajardo, ta ce cudanyar kasar ta da Sin ta fuskar kwallon kafa, na kara kusanto da sassan biyu zuwa ga juna, matakin da kuma zai haifar da moriya ga kasashen biyu.

Lucia Fajardo, ta ce tana fatan wasan kwallon kafa da kasar ta ta yi fice a kai, za ta samar da moriya ga kasuwannin wasanni na kasar Sin. Yayin zantawar ta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan, Lucia wadda ta kammala karatun digiri na 2 daga jami'ar Xiamen dake lardin Fujian, ta ce kasar ta na fatan raba fasahohin kwallon kafa da ta samu tare da Sin, musamman ma bangaren samar da horo ga yara kanana, da kuma kwarewa da sanin makamar aiki ta masu horas da 'yan wasa na Uruguay.

Ta kara da cewa "Da an ambaci 'Uruguay' da harshen Sinanci, muddin wanda ake Magana da shi ya san harkar kwallon kafa, za ka ji yace kasa ce mai kwarewa',". Lucia ta kara da cewa, Uruguay ta kuma shahara wajen cinikayyar nama.

Kwararriyar ta ce bayan da tawagar matasa ta 'yan kwallon kasar Uruguayan suka kai matsayi na 4, a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010 a Afirka ta kudu, sai kamfanonin sarrafa nama na kasar suka fara tallafawa kungiyar kwallon kafar ta Uruguay.

Kwararriyar ta ce Uruguay, wadda ta taba lashe kofin duniya na kwallon kafa sau 2, ta kuma lashe kofin zakarun yankin ta sau 15, tana kuma amfani da kwallon kafa a matsayin hanyar inganta alaka da kasar Sin, wadda kuma ita ce babbar abokiyar cinikayyar ta.

Tuni dai wasu yarjeniyoyin hadin gwiwa tsakanin sassan biyu suka ba da dama ga daruruwan 'yan wasan Uruguay, na samun horo a wasu manyan cibiyoyin wasanni na zamani dake Sin, baya ga tallafin kayayyakin wasanni da Sin din ke baiwa kasar Uruguay. A nata bangare kuwa, Uruguay na turowa sabbin makarantun wasa na kasar Sin masu horas da kwallon kafa, tana kuma karbar bakuncin kungiyoyin matasan 'yan wasan kwallo daga Sin.

Ciki irin wadannan makarantu na farko farko da aka bude, akwai makarantar Tangshan, dake lardin Hebei, ana kuma fatan sake bude karin wata makarantar a Guilin, dake jihar Guangxi Zhuang.

Duk da cewa al'ummar kasar Uruguay ba su wuce mutum kusan miliyan 3.4 ba, kuma kungiyoyin kwallon kafar ba su da yawa, a hannu guda, kungiyoyin na tafiya kafada da kafada da takwarorin su na turai, a fannin kulla dangantaka da kasar Sin.

Wani abun lura shi ne, kungiyoyin kwallon kafa na Uruguay wato "Nacional" da "Penarol", wadanda suka sha lashe gasannin zakarun kwallon kafa na kungiyoyin kasa da kasa sun kawo ziyara nan kasar Sin, amma kuma ya zuwa yanzu, ba wata kungiyar kwallon kafar kasar dake da ofishi a Sin. Yayin da a daya bangaren kungiyoyin dake buga gasar Bundesliga ta Jamus, ke da kungiyoyi abokan hulda a Sin da suka kai 8 zuwa 9, suna kuma da ofishi na musamman a kasar. Hakan a cewar Lucia Fajardo, ya baiwa kulaflikan na Jamus fifiko a wannan bangare. Ta ce ko shakka ba bu, Uruguay na bukatar samun wakilci na dindindin a Sin, kuma kwallon kafa za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hakan.

A yanzu haka dai Fajardo na karatun digiri na uku, a fannin tasirin shigar iyalai harkar kwallon kafar 'ya'yan su kanana a kasashen biyu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China