Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar Lagos ya yi kira da a kai zuciya nesa bayan zargin harbin masu zanga zanga
2020-10-21 20:58:16        cri
Gwamnan jihar Lagos dake kudancin Najeriya Babajide Sanwo-Olu, ya yi kira ga al'ummar jiharsa, da su kai zuciya nesa, biyowa bayan zargin harbin masu zanga-zanga da wasu mutane sanye da kayan sojoji suka yi, da almurun jiya Talata a yankin Lekki dake jihar.

Yayin wani jawabi ta gidan talabijin da gwamnan ya gabatar a yau Laraba, Babajide Sanwo-Olu, ya ba da umarnin dakatar da daukacin ayyukan hukuma a jihar na tsawon kwanaki 3, a matsayin wani mataki na nuna goyon baya ga masu zanga-zangar, wadanda ke rajin a rushe sashen rundunar 'yan sanda ta SARS mai yaki da 'yan fashi da makami.

Gwamnan ya kuma ce cikin kwanakin 3, za a sassauto da tutar kasar zuwa rabin sanda a dukkanin gine-ginen gwamnati, domin nuna alhinin halin da masu zanga-zangar suka shiga.

Kaza lika gwamnan ya ce, shi da 'yan tawagar sa, sun shafe daren jiya suna kewaya asibitocin dake jihar, domin samun cikakkun bayanai game da adadin mutanen da ko dai suka rasu, ko kuma suka jikkata.

Gwamna Sanwo-Olu, ya ce ya zuwa yammacin Talata, an samu masu zanga-zanga 28 da harbin bindiga, kuma daya daga cikinsu ya rasu a wani asibiti mai zaman kansa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China