Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: Kasashen Afrika sun yi gwajin cutar COVID-19 sama da miliyan 16
2020-10-22 09:46:43        cri

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar cewa, kasashen Afrika sun gudanar da gwaje gwajen cutar COVID-19 sama da miliyan 16.

Alkaluman baya bayan nan da Afrika CDC ta fitar ta ce, ta gudanar da gwaje gwajen cutar COVID-19 sama da miliyan 16, inda aka samu kashi 9.7 bisa dari sun kamu da cutar.

Ya zuwa ranar Laraba, adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 1,664,212, kamar yadda alkaluman Afrika CDC suka bayyana.

Afrika CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika AU, ta ce adadin mutanen da annobar ta kashe a nahiyar ya kai 40,222, ya zuwa ranar Laraba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China