Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafafen watsa labarain Afrika: Sin na ci gaba da jagorantar farfadowar tattalin arzikin duniya
2020-10-22 10:55:39        cri

Yayin da ake fama da annobar COVID-19, alkaluman tattalin arzikin kasar Sin a rubu'i na 3 na bana, sun ja hankalin kafafen watsa labarai na Afrika da dama.

Kafar yada labaran harkokin kasuwanci da na kudi ta Nairametrics ta Nijeriya, ta ruwaito cewa, alkaluman GDP na kasar Sin, sun karu da kaso 4.9 a rubu'i na 3 na bana, kuma farfadowar tattalin arzkin kasar ya samu karfi, kana yana ci gaba da jagorantar na duniya baki daya. Ta ce alkaluma daga kayayyakin da aka shigar tare da fitar da su daga kasar a watan Satumba da kayayyakin da aka daukewa haraji a tsibirin Hainan, sun nuna cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na kara karfi, yayin da masana'antu ke komawa bakin aiki. Ta kuma jaddada cewa, yadda aka samu tsayayyen tsarin aikin yi a kasar ya haifar da karin sayayyan kayayyaki a kasar.

Ita kuma kafar Daily Nation ta kasar Kenya cewa ta yi, tattalin arzikin kasar Sin ya farfado daga tasirin COVID-19, kuma ana sa ran zai zama tattalin arziki daya tilo mai karfi da zai samu ci gaba a bana.

Ta ce kasar Sin na gab da gudanar da taron baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shiga kasar daga ketare karo na 3 a birnin Shangahai, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin na da kwarin gwiwar komawa harkokin tattalin arziki bayan ta shawo kan annobar. Ya kuma nuna juriya da karfin tattalin arzikin kasar da cikakken goyon bayan da kasar ke ba tsarin huldar kasa da kasa da kuma bayyana manufarta ta bude kofa ga kasashen waje. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China