Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ECOWAS ta bukaci a shawo kan zanga-zangar kin jinin zaluncin 'yan sanda a Nijeriya
2020-10-23 11:14:04        cri

Kungiyar ECOWAS, mai raya tattalin arzikin yammacin Afrika, ta bukaci gwamnatin Nijeriya da masu zanga-zanga a kasar, su hau teburin sulhu domin gaggauta warware zanga-zangar adawa da zaluncin 'yan sanda da ake yi a fadin kasar, cikin lumana.

Wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua a jiya, ta ruwaito ECOWAS na kara kira ga dukkan masu zanga-zanga da su gudanar da shi cikin lumana, inda kuma ta bukaci hukumomin Nijeriya su gaggauta gudanar da bincike kan zaluncin na 'yan sanda da ake korafi.

Sanarwar ta kara da cewa, ECOWAS na kira ga gwamnatin Nijeriya, da matasa da kungiyoyin al'umma na kasar, su gaggauta tattaunawa domin warware matsalar da kuma kare mutuncin kasar a matsayin mai kiyaye doka da oda. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China