Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya bada umarnin dakatar da zanga zangar adawa da cin zalin 'yan sanda
2020-10-23 13:00:19        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bukaci matasan kasar dake zanga zangar nuna adawa da zalincin 'yan sandan kasar da su dakatar da zanga zangar, kana su rungumi matakan tattaunawa da gwamnati domin samun maslaha, shugaban ya yi kiran ne a yayin da ake samun karuwar tashin hankali a sassan kasar mafi yawan jama'a a Afrika.

Shugaba Buhari ya yi kiran ne a jawabin da ya gabatarwa 'yan kasar, inda ya jaddada cewa gwamnatin kasar tana cigaba da daukar matakan biyan bukatun da matasan kasar suka nema kuma tuni gwamnatin ta saurari kiraye kirayen nasu.

Shugaban Najeriyar ya gargadi masu zanga zangar da su guji lalata yanayin tsaron kasar da doka da oda, yana mai cewa, wannan lamarin ba abu ne da za a lamunta ba.

Cikin jawabin nasa, shugaba Buhari ya bukaci dukkan 'yan Najeriya da su koma harkokin kasuwancinsu, kana ya bukaci hukumomin tsaron kasar da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a 'yan kasa na gari masu bin doka da oda ba tare da an cutar da su ba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China