Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin MDD ya bukaci kasa da kasa su tallafawa yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Sudan da Sudan ta kudu
2020-10-23 13:14:04        cri

Wakilin musamman na babban sakataren MDD a yankin Kuryar Afrika, Parfait Onanga-Anyanga, ya bukaci kasa da kasa su tallafawa shirin yarjejeniyar fahimtar juna a tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu.

Cigaban kyautatuwar dangantaka a tsakanin Sudan da Sudan ta kudu, wata muhimmiyar dama ce game da yunkurin kasa da kasa na aikin wanzar da zaman lafiya, Onanga-Anyanga ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDD.

Onanga-Anyanga ya ce, kyakkyawar dangantaka tsakanin Sudan da Sudan ta kudu ya samar da muhimmiyar dama wadda kasa da kasa za su yi amfani da ita wajen karfafa tattaunawa da bangrorin biyu a yayin da suke fama da wasu kalubalolin na cikin gida, wanda ya kasance wani babban abin damuwa dake shafar huldar dake tsakanin kasashen biyu.

A Sudan ta kudu, har yanzu batun shirin wanzar da zaman lafiya yana fuskantar cikas kan muhimman batutuwa wadanda bangarorin kasar ke bukatar tallafi domin kaiwa zuwa ga mataki na gaba.

A nata bangaren, kasar Sudan, ta kama hanya mai bullewa, kana ta nuna aniyarta na amfani da matakan siyasa domin warware tarin matsalolin dake damun kasar. A halin yanzu, sama da kowane lokaci a baya, Sudan tana matukar bukatar taimako domin shawo kan dimbin matsalolin dake iya kawo cikas ga aniyar kafa gwamnati da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China