Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci a kara himma don warware batun yankin Abyei
2020-10-23 13:24:36        cri

Wakilin kasar Sin ya bukaci a dauki karin matakan kasa da kasa domin bin matakan siyasa don warware matsalolin dake shafar yankin Abyei wanda kasashen Sudan da Sudan ta kudu suke takaddama kansa.

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce, kasar Sin tana maraba da cigaba da daukar matakan daidaita tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu. Kasashen biyu sun bayyana aniyarsu na shiga matakin karshe na warware matsalolin dake shafar yankin Abyei, kuma kowane bangare ya nada jami'i mai kula da yankin.

Dai, ya fadawa kwamitin MDDr cewa, ya kamata kwamitin sulhun MDD ya mutunta shugabancin Sudan da Sudan ta kudu kan batun yankin na Abyei, kana ya karfafawa bangarorin biyu gwiwa da su cigaba da tuntubar juna, da yin tattaunawar kai tsaye.

Yace kasar Sin ta nuna damuwa matuka game da tashin hankalin da ake cigaba da samu game da yankin na Abyei, kuma ana fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa za su kai zuciya nesa su kaucewa daukar matakan da za su kara ruruta wutar rikici. Kasar Sin ta bukaci dukkan al'ummomin yankunan cikin gidan kasashen da su yi kokarin karfafa hanyoyin tuntubar juna a tsakaninsu da kuma tattaunawa a tsakanin shugabannin gargajiyar yankunan tare da taimakon MDD.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China