Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala baje kolin Canton Fair ta kafar intanet a lardin Guangdong na kasar Sin
2020-10-25 15:41:31        cri
A ranar Asabar an kammala bikin baje kolin shigi da ficin kayayyaki na kasar Sin karo na 128, wanda aka fi sani da Canton Fair, wanda aka gudanar ta kafar bidiyo a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

Xu Bing, kakakin baje kolin ya ce, bikin na kwanaki 10 ya ja hankalin kamfanonin cikin gida da na kasashen ketare kusan 26,000, inda aka baje kolin kayayyaki sama da miliyan 2.47, daga ciki akwai sabbin kayayyaki 730,000.

Masu sayen kayayyaki daga kasashe da shiyyoyin duniya sama da 226 ne suka mika bukatar neman halartar bikin baje kolin, tare da gudanar da shawarwarin ciniki, kamar yadda mashirya bikin suka bayyana.

A lokacin baje kolin, an gabatar da ayyuka kai tsaye ta intanet 284,800 wanda ya ja hankali masu kallo kusan miliyan 1.9, kana kamfanoni 2,046 sun yi amfani da hanyar fasahar bidiyo wajen tallata hajojinsu, wanda ya ja hankali masu ziyara sama da 160,000.

Wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da baje kolin ta hanyar intanet a wannan shekara sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Baje kolin wanda aka fara a shekarar 1957, an bayyana shi a matsayin wani muhimmin ma'auninn gwajin harkokin ciniki tsakanin kasar Sin da kasashen ketare. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China