Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi da takwaransa na Mali sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Mali
2020-10-25 16:13:43        cri

A yau Lahadi 25 ga wata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da ministan harkokin waje da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa na kasar Mali Moulaye, sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Mali.

Cikin sakon murnar Wang Yi, ya bayyana cewa, Mali daya ce daga cikin kasashen dake kudu da hamadar Sahara wadanda suka kulla huldar doplomasiyya da kasar Sin tun farkon kafuwarta, kuma a cikin wadannan shekaru 60, kasashen biyu sun nunawa juna sahihanci, sun kuma taimakawa juna, kana suna goyon bayan juna a harkokin kasa da kasa. Yanzu haka ana fama da matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, al'ummun kasashen Sin da Mali suna sanya kokori tare domin ganin bayan annobar cikin hanzari.

Wang Yi ya kara da cewa, yana son yin kokari tare da takwaransa na Mali domin tabbatar da sakamakon da aka cimma yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma taron kolin musamman da sassan biyu wato Sin da Afirka suka shirya domin dakile annobar COVID-19, tare kuma da ciyar da huldar hadin gwiwa mai sada zumunta dake tsakanin Sin da Mali gaba yadda ya kamata.

A nasa bangaren, Moulaye ya bayyana cewa, Mali da Sin suna da zumuncin gargajiya mai zurfi, har kullum suna gudanar da huldarsu cikin lumana a cikin shekaru 60 da suka gabata, bangaren Mali yana cike da imani cewa, huldar dake tsakaninsu za ta kara kyautatuwa a nan gaba, kuma Mali za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da kasar Sin take yi domin kiyaye 'yancin kasa da cikakken 'yancin yankunan kasa, ya kara da cewa, zai yi kokari tare da Wang Yi domin kara karfafa huldar hadin gwiwa dake taskanin kasashen biyu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China