Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin wallafa shirye-shirye kan yakin taimakawa Koriya ta Arewa wajen nuna turjiya kan zaluncin Amurka
2020-10-25 20:11:43        cri

A yau Lahadi an yi bikin kaddamar da shirye-shirye kan cika shekaru 70 da sojojin kasar Sin suka taimakawa Koriya ta Arewa wajen nuna turjiya kan zaluncin Amurka a nan birnin Beijing, wanda ya samu halartar mataimakin ministan ma'aikatar yada manufofin kasar Sin kuma shugaban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong.

Domin tunawa da cika shekaru 70 da sojojin kasar Sin suka taimakawa Koriya ta Arewa wajen turjewa zaluncin Amurka, CMG ya gabatar da shirya-shirye a jere ta rediyo da talabijin da kuma dandalin kafofin watsa labarai na zamani, alal misali "Yaran jarumai", da "Domin zaman lafiya", kuma ya gabatar da bikin wake-wake da raye-raye mai taken "yaran jarumai" domin tunawa da cika shekaru 70 da sojojin kasar Sin suka taimakawa Koriya ta Arewa wajen nuna turjiya kan zaluncin Amurka, duk wadannan sun jawo hankalin al'ummun kasar matuka, har yawan 'yan kallon sun kai biliyan 1.9, kana bisa bukatun 'yan kallo, babban kamfanin talabijin na kasa da kasa na kasar Sin zai wallafa fina-finai guda hudu mafiya samun karbuwa daga 'yan kallonsu a kasashen ketare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China