Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan Najeriya sun kaddamar da shirin kakkabe muggan laifuka a lokacin zanga zanga a duk fadin kasar
2020-10-25 20:44:14        cri
Hukumar 'yan sandan Najeriya tace ta kaddamar da wani shirin kakkabe dukkan ayyukan bata gari a duk fadin kasar domin samun zaman lafiya a kasar, bayan samun wasu rahotanni dake nuna cewa wasu 'yan bata gari da ake zargin suna fakewa karkashin masu zanga zangar suna kwashe kayayyakin jama'a tare da lalata dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu.

Frank Mba, kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya, ya fada cikin wata sanarwa a birnin Abuja cewa, tuni hukumar 'yan sandan Najeriyar ta baza jami'anta domin kare dukiyoyi da kuma kawo karshen tashe tashen hankula a sassan kasar.

Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mutane 69 ne aka kashe a lokacin zanga zangar neman kawo karshen gallazawar 'yan sandan kasar.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya bayyana wa tsoffin shugabannin kasar alkaluman a lokacin wani taron da ya gudanar da tsoffin shugabannin kasar ta kafar bidiyo da nufin lalibo bakin zaren warware matsalar tsaron da ke damun kasar.

A lokacin da yake gabatar da jawabi ga tsoffin shugabannin Najeriyar, shugaba Buhari yace, abin takaici ne yadda matasan suka fara zanga zangarsu cikin lumana don nuna adawa da rundunar 'yan sandan musamman masu yaki da fashi da makami wato SARS, amma wasu bata gari sun kwace ragamar zanga zangar suka dinga aikata barna.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China