Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 20:12:19    
Tattalin arziki na masana'antun Sin zai samu kyautatuwa

cri
A ranar 5 ga wata, a nan birnin Beijing, ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ta Sin da cibiyar nazarin zamantakewar al'umma ta Sin sun ba da rahoto na yanayin kaka kan sha'anin samun bunkasuwar tattalin arziki na masana'antun kasar Sin na shekarar 2009, inda aka bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, tattalin arziki na masana'antun kasar Sin zai samu kyautatuwa.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, babban injiniya na ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ta Sin Zhu Hongren ya ce, a farkon watanni 9 na wannan shekara, yawan karuwar kudin da masana'antun Sin suka samu ya kai kimanin kashi 8.7 cikin kashi 100, daga watan Yuli zuwa watan Satumba, yawan karuwar tattalin arziki a fannin samun bunkasuwar masana'antu ya karu da sama da kashi 10 cikin kashi 100 a watanni 4. An kimanta cewa, daga watan Oktoba zuwa watan Disamba, yawan karuwar tattalin arziki na masana'antun kasar Sin zai kai kimanin kashi 15 cikin kashi 100 ko kashi 16 cikin kashi 100.

Zhu Hongren ya ce, a shekarar 2010, sakamakon daukan matakai na hakika da Sin ta yi wajen aiwatar da manufofin kudi masu sassauci, sha'anin saka jari a kan harkokin masana'antu zai cigaba da samun bunkasuwa, kuma matakan sa kaimi ga sha'anin sayayya da kara yawan bukatun sayayya a gida zai kara tabbatar da yawan sayayya a gida. Kana a karkashin yanayi na samun kyautatuwar tattalin arziki a fadin duniya, a shekara mai zuwa, kayayyakin masana'antu da Sin za ta fitar za su ci gaba da samun bunkasuwa, a sakamakon haka, a badi, tattalin arziki na masana'antun Sin zai samu kyautatuwa.(Bako)