Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 20:05:16    
Sojojin kasar Sin za su ci gaba da yin kokari wajen samar da zaman karko da zaman lafiya a shiyyoyi da kasashen duniya

cri

Ministan tsaro na kasar Sin babban janar Liang Guanglie ya bayyana a ran 6 ga wata a birnin Beijing cewa, sojojin kasar Sin za su ci gaba da yin kokari wajen samar da zaman karko da zaman lafiya a shiyyoyi da kasashen duniya.

Domin taya murnar cikon shekaru 60 na kafuwar rundunar mayakan sama na kasar Sin, an shirya dandalin tattaunawa a tsakanin kasa da kasa kan samun zaman lafiya da bunkasuwar rundunar mayakan sama a ran 6 ga wata a birnin Beijing.

Mr. Liang ya yi wani jawabi na cewa, sojojin kasar Sin za su ci gaba da aiwatar da manyan tsare tsare na tsaron kai cikin yakini, da kuma yin kokari tare da sojojin kasashen duniya wajen kiyaye zaman lafiya da zaman lumana a duk duniya.

Liang ya ce, sai da kara fahimtar juna da amincewa da juna da hadin kai ne kawai, za a iya sa kaimi ga mayakan sama na kasa da kasa su yi kokari tare wajen cimma burin samun zaman lafiya. Shugabannin mayakan sama na kasa da kasa sun tattauna a birnin Beijing kan burinsu na samar da zaman lafiya, da kuma kyakkyawar makomar bunkasuwar mayaka, wannan zai sa a kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin mayakan sama na kasa da kasa, haka kuma zai yi amfani ga yunkurin kiyaye zaman lafiya a sararin samaniya.(Danladi)