Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 21:09:49    
Firaministan Sin Wen Jiabao ya isa birnin Alkahira

cri
A ranar 6 ga wata, firaministan Sin Mr. Wen Jiabao ya isa birnin Alkahira kuma zai fara ziyarar aiki a hukunce a kasar Masar da halartar taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Sharm El Sheikh. Firaministan kasar Masar Ahmed Mahmoud Mohamed Nazef ya yi masa kyakkyawar tarba a babban filin jiragen sama.

A cikin jawabin da firaminista Wen Jiabao ya yi a babban filin jiragen sama, ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 10 da kafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kasar Masar. Kasar Sin tana fatan yin amfani da wannan dama, domin kara kyautata da inganta hakikanin hadin gwiwa daga dukkan fannoni tsakaninsu, da inganta shawarwari da hadin gwiwa wajen daidaita lamuran duniya da na shiyya-shiyya da tabbatar da taron dandalin tattaunwar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da ta Masar da kuma dukkan kasashen Afrika baki daya, domin kara kiyaye moriyar kasashen biyu da kuma moriyar dukkan kasashe masu tasowa, ta hakan, za a iya sa kaimi da aikin shimfida zaman lafiya a yankin kasashen Afrika da kuma dukkan duniya baki daya.

A yayin ziyararsa, firaministan Wen zai yi shawarwari da shugaban kasar Masar Muhammed Hosni Mubarak da firaministan kasar Ahmed Mahmoud Mohamed Nazef, kuma Sin da kasar Masar za su daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tsakaninsu. Kana, zai kai ziyara a cibiyar kawancen kasashen Larabawa da ke birnin Alkahira.

Ya yi imani da cewa, ziyararsa za ta kyautata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da Masar da samar da sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zuwa wani sabon matsayi.(Bako)