Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 16:24:09    
Hu Jintao ya isa birnin Kuala Lumpur

cri

Bisa gayyatar da shugaban kasar Malaysia Tuanku Mizan Zainal Abidin ya yi masa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Kuala Lumpur babban birnin kasar Malaysia a ran 10 ga wata don fara yin rangadi a kasar.

Wannan ne karo na farko da Hu Jintao ya ziyarci kasar Malaysia bayan da ya hau kan karagar mulkin kasar Sin, kuma wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kawo wa kasar ziyara bayan shekaru 15 da suka gabata.

Hu Jintao ya bayar da jawabi a rubuce a filin saukar jiragen sama, inda ya nuna farin ciki ga bunkasuwar huldar dake tsakanin Sin da Malaysia. Ya bayyana cewa, kasashen Sin da Malaysia dukkansu kasashe ne masu tasowa ne na yankin Asiya da tekun Pacific, suna cin moriya iri bai daya a fannoni da yawa. Zurfafa hadin gwiwarsu a cikin sabon halin da ake ciki ya dace da cin moriyar dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu da jama'arsu, kana zai kawo moriya ga shimfida zaman lafiya da kara zaman wadata a yankin. Yana fatan za a kara fahimtar juna da kara dakon zumuncinsu da karfafa hadin gwiwarsu na cin moriyar juna a yayin wannan ziyara don ingiza bunkasuwar huldar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.(Lami)