Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-07 19:28:53    
Kasar Sin ta riga ta zama wata muhimmiyar aminiyar cinikayya ta kasashen Afrika

cri
Ministan harkokin waje na kasar Brundi Angustin Nsanze ya bayyana kafin taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika cewa, matakai guda takwas da gwamnatin kasar Sin ta sanar a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika da aka shirya a shekaru uku da suka wuce, sun inganta karuwar jarin cinikayya da ake zubawa ga juna tsakanin Sin da kasashen Afrika, yanzu kasar Sin ta riga ta zama wata muhimmiyar aminiyar cinikayya ta kasashen Afrika.

Har wa yau kuma, mai ba da shawara kan harkokin waje na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Morocco Farida Jaidi, wanda ke halartar taron manyan jami'ai a karo na 7 na dandalin tattaunawa kan hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika da ake yi a birnin Sharm el-Sheikh, ya bayyana cewa, hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika na da ma'ana sosai. Yanzu, ana kara habaka hadin kai tsakanin bangarorin biyu. Kasar Sin na yin kokari da nufin taimakawa babban yankin Afrika don tabbatar da burin samun bunkasuwa. Ta ayyuka daban daban da aka yi tsakanin Sin da kasashen Afrika, ana iya ganin cewa, kasar Sin na fatan karfafa hadin kai tsakaninta da Afrika da zuciya daya. Kasar Sin ta samar da taimako masu yawa ga kasashen Afrika, jama'ar kasashen Afrika kuma suna bukatar taimakon irin nan cikin gaggawa. (Bilkisu)