Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 15:17:40    
Shigar Amurka a cikin bikin baje-kolin duniya na birnin Shanghai ta bayyana bunkasuwar dangantaka tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata

cri
A ran 9 ga wata, wakiliyar musamman ta majalisar gudanarwar Amurka mai kula da dangantakar hadin gwiwa a duniya Elizabeth Bagley ta bayyana cewa, shigar Amurka a cikin bikin baje-kolin duniya na birnin Shanghai ta bayyana bunkasuwar dangantaka tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.

Bagley ta bayyana a taron manema labaru a game da batun shigar Amurka a cikin bikin baje-kolin duniya na birnin Shanghai da aka yi a majalisar gudanarwar Amurka cewa, Sin ta nuna goyon baya ga Amurka da ta shiga bikin baje-kolin duniya na birnin Shanghai, shigar Amurka wata muhimmiyar shaida ce, wadda ta bayyana bunkasuwar dangantaka tsakanin bangarorin biyu da huldar cinikayya tsakaninsu yadda ya kamata.

Bagley ta bayyana cewa, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton za ta kai ziyara a dakin nune-nune na Amurka na bikin baje-kolin duniya da ke a birnin Shanghai a ran 15 ga wata yayin da take ziyara a kasar Sin.

Majalisar gudanarwar Amurka ta gabatar da wata sanarwa a kwanakin baya, inda ta ce, tawagar Amurka tana son yin amfani da damar shiga cikin bikin baje-kolin duniya don zurfafa zumunci tsakanin jama'ar Sin da ta Amurka, da bayyana alkawarinta na raya dangantaka tsakaninta da kasar Sin.(Zainab)