http://big5.cri.cn/gate/big5/www.beijing-olympic.org.cn/
Janairu, 2006 / Home / Sin Ciki da Waje / Email Us /Print this page

Gabatarewa:


A farkon lokaci na karnin da muke ciki, halin da ake ciki a duk duniya yana ta samun sauye-sauye sosai, yunkurin raya duk duniya bai daya ma yana ta samun karfafuwa. Amma har yanzu zaman lafiya da neman bunkasuwa muhimman batuttuwa ne ga lokacin da ake ciki. Kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa da kara yin hadin guiwa kyakyawan fata daya ne na jama'ar duk duniya bisa bayanan tarihi da ba za a iya hanawa ba. Bugu da kari kuma, abubuwan da ke haddasa rudani da rashin tabbas a cikin harkokin kasa da kasa suna ta karuwa. Matsalolin zaman karko iri iri suna nan tare. Har yanzu ba a warware maganar zaman lafiya ba tukuna, amma maganar neman bunkasuwa ta fara jawo hankulan mutane sosai...
[ A kara karfin hadin guiwa tsakanin Sin da Afrika daga duk fannoni] [Saurari]

Babi na farko:
Matsayin kasashen Afrika da amfaninsu
Babi na biyu:
Huldar dake tsakanin kasar Sin da Afrika
Babi na uku:
Manufar da kasar Sin take tafiya kan Afrika
Babi na hudu:
Za a karfafa hadin kai daga duk fannoni a tsakanin Kasar Sin da Afrika
[1] Harkokin siyasa
[2] Tattalin arziki
[3] A fannonin ba da ilmi da kimiyya da al'adu da kiwon lafiya da kuma zaman al'umma
[4] Zaman lafiya da kwanciyar hankali
Babi na biyar:
Taron dandalindandalin hadin kai na Sin da Afrika da kuma aikace-akace nan gaba
Babi na shida:
Dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kungiyoyi na shiyyar Afrika
Gabatarewa:   Kai Sama


A farkon lokaci na karnin da muke ciki, halin da ake ciki a duk duniya yana ta samun sauye-sauye sosai, yunkurin raya duk duniya bai daya ma yana ta samun karfafuwa. Amma har yanzu zaman lafiya da neman bunkasuwa muhimman batuttuwa ne ga lokacin da ake ciki. Kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa da kara yin hadin guiwa kyakyawan fata daya ne na jama'ar duk duniya bisa bayanan tarihi da ba za a iya hanawa ba. Bugu da kari kuma, abubuwan da ke haddasa rudani da rashin tabbas a cikin harkokin kasa da kasa suna ta karuwa. Matsalolin zaman karko iri iri suna nan tare. Har yanzu ba a warware maganar zaman lafiya ba tukuna, amma maganar neman bunkasuwa ta fara jawo hankulan mutane sosai.

Kasar Sin kasa mai tasowa ce mafi girma a duk fadin duniya. Tana neman bunkasuwa cikin lumana, kuma tana bin manufar diplomasiyya ta zaman lafiya da manufofin diplomasiyya na ra'ayin kanta. Kasar Sin tana fatan za ta iya kafa kuma da raya dangantakar sada zumunta a tsakaninta da dukkan sauran kasashen duniya bisa ka'idoji 5 na zaman tare cikin lumana domin ta iya kara aminci da hadin guiwa a tsakaninta da sauran kasashe wajen domin tabbatar da zaman lafiya da na karko da bunkasuwa a duk duniya.

Afirka nahiya ce da take da kasashe masu tasowa mafi yawa, kuma wata muhimmiyar karfi ce ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa a duk duniya. A cikin sabon halin da ake ciki, dangantakar sada zumunta irin ta gargajiya da ke kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka tana fuskantar sabuwar damar neman bunkasuwa. A cikin halin da ake ciki, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta tsara kuma ta bayar da wannan Takardar Manufofin da take bi kan Afirka shi ne ta bayyana burin da za ta cimma da hanyar cimma su da kuma manufofin da take dauka kan Afirka. Haka nan kuma ta bayar da shawarar shirin yin hadin guiwa a tsakanin bangarorin 2 daga duk fannoni a nan da wasu lokuta masu zuwa. A sakamakon haka, za a iya raya dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da Afirka cikin dogon lokaci mai zuwa kuma cikin hali mai dorewa. Bugu da kari kuma, hadin guiwa irin ta moriyar juna a tsakaninsu za ta iya kai zuwa wani sabon mataki a kai a kai.
 
 
  Babi na farko: Kai Sama
Matsayin kasashen Afrika da amfaninsu

Babban yankin Afrika yana da dogon tarihi, kuma yanki na da fadi, kuma an kasance da albarkatai da yawa, ta haka ne akwai babban karfin neman samun bunkasuwa sosai. Bayan da jama'ar kasashen Afrika suka yi fama cikin dogon lokaci, har sun kubutar da kansu daga mulkin mallaka da kuma rushe tsarin wariyar kabila, har kasashen Afrika sun kawo babban taimako ga ci gaban wayin kai na ‘Dan Adam.

Bayan da kasashen Afrika suka samu mulkin kai, sai tare da nuna himma ne sun yi aikin wurjanjan don neman samu wata hanyar samu bunkasuwa har da hada kansu don neman zaman lafiya da zama mai dorewa da ci gabansu.Bisa kokarin da kasashe daban daban na Afrika da kuma kungiyar hada kan Afrika da kawancen kasashen Afrika suke yi tare, yanzu babban halin da ake ciki a kasashen Afrika yana da kyau, kuma a kai a kai ne hargitsin dake tsakanin kasa da kasa na wasu wurare suna nan suna samu daidaituwa, Bugu da kari kuma tattalin arzikinsu ya sami bunkasuwa a shekara daya bayan daya. Sabon shirin neman bunkasuwa na kasashen Afrika ya kawo babban makoma mai kyau. Kuma tare da himma ne kasashen Afrika suke yin hadin guiwa a tsakanin kudu da kudu da ingiza tattaunawar da ake yi tsakanin kudu da arewa, har an kawo babban taimako cikin harkokin duniya.

Amma, har yanzu dai ci gaban kasashen Afrika yana fuskantar kalubale, muddin kasashen Afrika su ci gaba da yin kokari da kuma samu goyon baya daga kasashen duniya,tabbas ne a cikin sabon karni, kasashen Afrika za su iya haye wahalhalu da samu wadatuwa sosai.

  Babi na biyu:   Kai Sama
Huldar dake tsakanin kasar Sin da Afrika

Zumuncin dake tsakanin kasar Sin da Afrika dadadde ne kuma yana da harsashi mai karfi . Kasar Sin da Afrika suna kasance da makamancin tarihi . A cikin gwagwarmayar neman ‘yancin al'umma sun nuna jin kai ga juna kuma sun goyi bayan juna . Saboda haka sun sada zumunci kwarai da gaske a cikinsu .

Kafuwar sabuwar kasar Sin da samun mallakar kan kasashen Afrika sun fara sabon karni kan huldar da ke tsakanion kasar Sin da Afrika . A cikin shekaru fiye da 50 da suka shige huldar siyasa da ke tsakanin bangarorin biyu tana da inganci . Shugabannin kasar Sin da na Afrika sun kai wa juna ziyara . Ma'amalar tsakanin jama'ar bangarorin biyu ta kara yawa . Huldar tattalin arziki da ciniki ta sami yalwatuwa da saurin gaske . Hadin gwiwar da suka yi a sauran fannoni kuma ya sami sakamako sosai . A cikin harkokin duniya sun karfafa tattaunawa da sulhuntawa . Kasar Sin ta ba da taimako ga kasashen Afrika bisa karfinta . Kasashen Afrika kuma sun ba da goyon baya mai karfi ga kasar Sin .

Sahihancin zumunci da zaman daidai wa daida da hadin gwiwa da samun yalwatuwa tare ka'idoji ne na ma'amala da hadin kai na tsakanin Sin da Afrika kuma karfi ne da ya ingiza ci gaban dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Afrika.

 
  Babi na uku:   Kai Sama
Manufar da kasar Sin take tafiya kan Afrika

Kara karfin hadin kai da yin aikatayya tare da kasashen Afrika wannan shi ne wani muhimmin kashi dake cikin manufar harkokin waje da kasar Sin take tafiyar da ita wajen neman mulkin kai da zaman lafiya. Ba tare da tangadawa ba, kasar Sin za ta ci gaba da yada al'adar yin zumunci tare da kasashen Afrika, bisa babbar moriya ta jama'ar kasar Sin da ta jama'ar kasashen Afrika, za a kulla sabuwar dangantakar abokantaka tare da kasashen Afrika bisa matsayin neman daidaicin siyasa da nuna wa juna aminci da kuma neman bunkasuwar tattalin arziki tare da yin musanye musanyen al'adu tsakanin sassa biyu. Babbar ka'idar da babban makasudin da kasar Sin take nemawa kan manufarta ga kasashen Afrika su ne:

Nuna sahihanci da amincewa da yin zaman daidai wa daida. Da nacewa bin ga ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana da nuna girmamawa ga kasashen Afrika bisa hanyoyinsu na neman bunkasuwa da kai goyon baya ga kasashen Afrika wajen hadin guiwa da samun babban karfi.

Kai wa juna moriya da neman samun bunkasuwa tare. Da nuna goyon baya ga kasashen Afrika wajen neman bunkasuwar tattalin arziki da gina kasashensu da kyau, kuma ta hanyoyi daban daban ne za a kara yin hadin guiwar tattalin arziki da ciniki neman ci gaban zaman al'umma don samu bunkasuwa tare.

Da kuma kai wa juna goyon baya da yin hadin guiwa sosai.Da kara yin aikatayya tare da kasashen Afrika da nuna goyon baya wa juna da neman adalci sosai, da ci gaba da ingiza kasashen duniya da su kara nuna muhimmanci ga zaman lafiya da bunkasuwa na kasashen duniya.

Za mu koyi juna da neman bunkasuwa tare da kara yin hadin guwai kan kimiyya da kiwon lafiya da neman wata hanyar neman bunkasuwa tare.

Sin Kasa daya shi ne babban tushen siyasar neman bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashe ko kungiyoyi na Afrika. Gwamnatin kasar Sin ta nuna yabo ga yawacin kasashen Afrika da su bi ka'idar Sin kasa daya kawai, kuma ba su yi neman bunkasa dangantakar hukuma tare da yankin Taiwan ko yin ma'amala bisa hukumar Taiwan, da kuma nuna goyon baya ga babban sha'anin dikuwar kasar Sin, Bisa tushen Sin kasa daya kawai ne kasar Sin take son neman kulla huldar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen da ba su kulla tare da mu tukuna da neman bunkasa dangantakar dake tsakanin kasa da kasa.

  Babi na hudu:   Kai Sama
Harkokin siyasa


(1)
  Mu'amalar shugabanni

Za a kiyaye yunkurin kai wa juna ziyara da tattaunawa a tsakanin shugabannin kasar Sin da na kasashen Afrika.

(2) Mu'amalar majalisun dokokin kasa

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisun kasashe daban daban na Afrika za su kara ma'amalar zumunci ta hanyoyi daban daban bisa tushen girmama wa juna da karfafa fahimta da yalwata hadin kai .

(3) Mu'amalar tsakanin jam'iyyun siyasa

Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta yi ma'amala ta hanyoyi daban daban da jam'iyyu da kungiyoyin siyasa masu abuta na kasashe daban daban na Afrika bisa harsashen mulkin kai da zaman daidai wa daida da girmama wa juna da rashin tsoma baki cikin harkokin juna don kara fahimta da zumunci da neman amincewa da hadin gwiwa.

(4) Tsarin yin tattaunawa

Za a kafa kuma da kara kyautata kwamitin bangarori 2 da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da tsarin yin tattaunawa kan harkokin siyasa a tsakanin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da ma'aikatun harkokin waje na kasashen Afirka da hadadden kwamitin yin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya da hadadden kwamitin yin hadin guiwar kimiyya da fasaha da dai sauransu. Kasar Sin da kasashen Afirka suna yin amfani kuma da raya tsarin yin tattaunawa ne bisa halin da ake ciki a duniya kuma maras alkibla.

(5) Yin hadin guiwa kan harkokin duniya

Za a ci gaba da kara yin hadin guiwa da gama kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kan harkokin duniya, kuma za su kara yin musayar ra'ayoyinsu da daidaita matsayin da suke dauka kan wasu muhimman maganganun duniya da na yankuna daban-dabam. A kan wasu muhimman maganganun da ke shafar ikon mulkin kasa da cikakken yankunan kasa da martabar al'umma da maganar kare hakkin Adam, kasar Sin da kasashen Afirka za su nuna wa juna goyon baya. Kasar Sin tana kuma nuna goyon baya ga kasashen Afirka kan yadda za su halarci al'amuran duniya cikin halin daidai wa daida. Haka nan kuma za su yi kokari tare wajen girmama gudunmawar Majalisar Dinkin Duniya da ainihin ka'dojin tsarin Majalisar Dinkin Duniya. Sannan kuma za su yi kokari tare wajen kafa wani sabon tsarin tattalin arziki da na siyasa na duniya cikin adalci bisa ka'idojin zaman daidai wa daida da moriyar juna. Bugu da kari kuma, za su yi kokari tare kan yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin kasashe daban-dabam bisa dokokin kasa da kasa tare da dimokuradiyya domin kiyaye moriyar halal ta kasashe masu tasowa.

(6) Yin musanye-musanye a tsakanin gwamnatocin da ba na tsakiya ba

Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana mai da hankali kwarai kan yadda kananan hukumominta da na kasashen Afirka suke yin mu'ammala. Tana kuma nuna goyon baya ga yunkurin kafa dangantakar sada zumunta a tsakanin larduna da birane na kasar Sin da na kasashen Afirka. Bugu da kari kuma, tana sa kaimi ga bangarorin biyu da su yi musanye-musanye da hadin guiwa a tsakaninsu kan maganar neman bunkasuwar wurare daban-daban na kasar Sin da na kasashen Afirka.

Tattalin arziki


(1) Cinikayya

Gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai masu yakini don samar da sauki ga kara shigar da kayayyakin kasashen Afrika cikin kasuwannin kasar Sin, kuma cikin tsanaki ne za ta aiwatar da aikin ba da gatanci ga kasashe mafiya talauci na Afrika wajen fitar da hajojinsu zuwa kasar Sin ta yadda za a habaka da kuma samar da daidaici ga cinikayyar da ke tsakanin bangarorin biyu da kuma kyautata tsarin cinikayya. Ta hanyar shawarwari cikin lumana a tsakanin bangarori da yawa da kuma tsakanin bangarori biyu , su yi hakuri da juna da kuma rangwame da kuma daidaita sabanin da ke tsakaninsu wajen yin cinikayya yadda ya kamata. Sa'anann kuma ta sa kaimi ga rukunonin masana'antu na bangarorin biyu wajen kafa hadadiyyar masana'antu da kasuwanci da ke tsakaninta da kasashen Afrika. Kasar Sin tana son yin shawarwari da kuma daddale yarjejeniyar yin cinikayya cikin ‘yanci a tsakaninta da kasashen Afrika da kungiyoyin shiyya shiyya bisa sharadin da ya nuna.

(2) Zuba jari

Gwamnatin kasar Sin ta himmantar da masana'antunta wajen zuba jari da farfado da sha'aninsu a kasashen Afrika, kuma za ta ci gaba da samar da rancen kudi bisa gatanci da samar da lamuni ga wadanda suke sayen kayayyakin fici na kasar Sin , kuma tana son yin bincike kan sabuwar hanya da dabarar da za a bi tsakaninta da kasashen Afrika don ciyar da hadin guiwar zuba jari gaba. Tana ci gaba da tsara da kuma kyautata manufofin da abin ya shafa da kuma kara karfafa jagorancinta da mai da hankali sosai ga samar da hidima da sauki. Tana maraba da masana'antun kasashen Afrika da su zuba jari a kasar Sin. Tana ci gaba da yin shawarwari a tsakaninta da kasashen Afrika don rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ke tsakanin bangarorin biyu wajen sa kaimi da kiyaye jarin da aka zuba da yarjejeniyar kawar da harajin da bangarorin biyu suke bugawa gaba daya da kuma aiwatar da su, za ta kago kyakyyawan muhallin yin hadin guiwar zuba jari tare da kasashen Afrika da kuma kiyaye moriyar halal na masu zuba jari na bangarorin biyu.

(3) Yin hadin guiwa wajen harkokin kudi

Cikin himma da kwazo ne ake yalwata huldar hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen harkokin kudi. Gwamnatin kasar Sin tana nuna goyon baya ga hukumominta na kula da harkokin kudi don su kara yin ma'amala da hadin guiwa a tsakaninsu da na kasashen Afrika da na shiyya shiyya.

(4 ) Yin hadin guiwa wajen aikin noma

A ci gaba da yin hadin guiwa da ma'amala a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen sha'anin noma ta hanyar matakai da hanyoyi da samfurori da yawa.Muhimmin aiki shi ne kara hadin guiwar tsakaninsu wajen yin amfani da gonaki da shuka shuke-shuken gona da kuma yin amfani da fasahar kiwon dabbobi da kara ingancin abinci da kera na'urorin noma da gyara amfanin gona da dai sauran fannoni. A kuma kara karfin yin hadin guiwar fasahohin noma da ba da horo wajen yin amfani da fasahar noma cikin himma da kwazo, da kuma kafa ayyuka masu ba da misali ga aikin gwajin fasahar noma a kasashen Afrika. Sa'anan kuma a kara saurin tsara shirin hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wajen sha'anin noma.

(5) Yin muhimman gine-gine

Kara yin hadin gwiwa a fannin zirga-zirga da na sadarwa da na aikin tsare ruwa da na karfin lantarki da sauran fannonin muhimman gine-gine. Gwamnatin kasar Sin ta nuna cikakken goyon bayanta ga masana'antun kasar Sin da su shiga ayyukan yin muhimman gine- gine na kasashen Afirka, da kara kulla kwangiloli tare da kasashen Afirka bisa babban mataki, da kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin gefuna da yawa ko tsakanin gefuna 2 wajen kulla kwangila tare da kasashen Afirka sannu a hankali. Da kara yin hadin gwiwa wajen fasaha da sarrafa harkokin masana'antu, kuma a mai da hankali don ba da taimako ga kasashen Afirka domin kara kwarewarsu wajen bunkasa kasashensu.

(6) Hadin gwiwa wajen albarkatun kasa

Kara yin mu'amala da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen albarkatun kasa da sadarwa. Gwamnatin kasar Sin ta himmantu da nuna goyon baya ga masana'antu masu karfi na kasar da su bi ka'idar samun moriyar juna da samun bunkasuwa tare, kuma su yi hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyoyi da yawa domin aiwatar da albarkatun kasa tare da yin amfani da su bisa gaskiya, da taimaka wa kasashen Afirka don su mai da matsayi mai rinjaye wajen albarkatun kasa ya zama matsayi mai rinjaye wajen yin gasa, da sa kaimi ga kasashe da shiyyoyin Afirka da su tabbatar da ci gaba da samun ci gaba mai dorewa.

(7) Hadin gwiwa wajen sha'anin yawon shakatawa

Gwamnatin kasar Sin ta himmantu ga tafiyar da aikin kimkimtsa jama'ar kasar Sin don su yi yawon shakawata a wasu kasashen Afirka cikin kungiya-kungiya, kuma bisa bukatu da hakikanin halin da ake ciki a kasashen Afirka, za ta kara sa kasashen Afirka da yawa cikin “wuraren da jama'ar kasar Sin suke yin yawon shakatawa a kasashen waje cikin kungiya-kungiya”. Kasar Sin kuma tana maraba da zuwan jama'ar kasashen Afirka don yin yawon shakatawa a kasar.

(8) Rage ko kuma soke bashi

Gwamnatin kasar Sin tana son ci gaba da taimaka wa kasashen Afirka domin daidaita da kuma rage yawan basussukan da suka ci daga wajenta ta kasar Sin ta hanyar yin shawarwari cikin aminci. Kuma za ta ci gaba da yin kira ga kasashen duniya musamman ma kasashe masu sukuni da su kara daukar hakikanan matakai da yawa kan matsalar rage ko kuma soke basussukan da kasashen Afirka suka ci daga wajen su.

(9) Gudummawar tattalin arziki

Bisa halin da gwamnatin kasar Sin take ciki wajen kudi da raya tattalin arziki, za ta ci gaba gabatar da kuma kara ba da gudummawa ga kasashen Afirka gwargwadon karfinta kuma ba tare da sharadin siyasa ba.

(10) Hadin gwiwa tsakanin gefuna da yawa

Gwamnatin kasar Sin za ta kara yin shawarwari da samun daidaituwa tsakaninta da kasashen Afirka wajen tattalin arziki da ciniki da ake yi tsakanin gefuna da yawa, da hukumomi da tsarin kudi, da sa kaimi ga M.D.D. da sauran kungiyoyin kasashen duniya don su kara mai da hankali kan matsalar bunkasuwa, da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin kudu da kudu, kuma ga kafa tsarin cinikayya mai adalci kuma bisa gaskiya tsakanin gefuna da yawa, da kara samun ikon yin jawabi da tsai da kuduri na kasashe masu tasowa cikin harkokin kudi na kasashen duniya. Gwamnatin kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashe da kungiyoyin kasashen duniya domin nuna goyon baya ga bunkasa kasashen Afirka tare, da ba da taimako domin tabbatar da makasudin bunkasa Afirka cikin shekaru duba daya.

 
A fannonin ba da ilmi da kimiyya da al'adu da kiwon lafiya da kuma zaman al'umma Kai Sama


(1) Hadin gwiwa a wajen horar da kwararru da ba da ilmi

kasar Sin za ta ba da taimako don ganin cewa ‘asusun horar da kwararru a Afirka' da gwamnatin kasar Sin ta kafa za ta ba da cikakken amfaninsa kamar yadda ya kamata, kuma za ta gano muhimman abubuwan da ya kamata a mai da hankali a kansu da habaka fannonin da bangarorin biyu za su hada gwiwa da kara tallafawa juna bisa hakikanan bukatun kasashen Afirka.

Za a ci gaba da tura wa juna dalibai tsakanin Sin da kasashen Afirka. Gwamnatin kasar Sin za ta kara yawan daliban da za su sami sukolashif daga wajenta kamar yadda ya kamata, kuma za ta ci gaba da aikawa da malamai zuwa Afirka don su ba da taimako. Za ta kuma taimaka wa kasashen Afirka a wajen koyar da Sinanci. Za ta aiwatar da ayyukan ba da taimako a Afirka a fannin ba da ilmi, don sa kaimi ga bunkasa aikin ba da ilmi na Afirka a fannonin da ba su da karfi sosai. Ban da wannan, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannonin ba da ilmin sana'a da ba da ilmi daga nesa da kuma sa kaimi ga hukumomin ba da ilmi na bangarorin biyu da su yi mu'amala da hadin gwiwa tsakaninsu

(2) Hadin gwiwar kimiyya da fasaha

Bisa ka'idar girmama juna da taimakon juna da samun moriya tare, kasar Sin za ta yi kokarin ingiza hadin gwiwa tsakaninta da Afirka a fannonin nazari da bunkasa fasahohi da kuma musanyarsu da kuma karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin ayyukan gona da yin amfani da hasken rana da binciken yanayin kasa da haka kwal da nazarin sabbin magunguna da dai sauransu wadanda bangarorin biyu ke da bukatu iri daya. Ban da wannan, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da shirin horar da kwararrun Afirka a fannin fasaha da kuma shirye-shiryen gwaji a fannin ba da taimakon fasaha, za ta kuma yi kokarin wanzar da sabbin fasahohi a kasashen Afirka.

(3) Musayar al'adu

kasar Sin za ta tabbatar da yarjejeniyoyin da ta daddale tare da kasashen Afirka a fannin al'adu, kuma za ta tabbatar da tuntubar juna a kullum a tsakanin hukumomin al'adu na bangarorin biyu, haka kuma za ta kara musanye-musanye tsakanin masu ayyukan fasaha da ‘yan wasa na bangarorin biyu. Bisa bukatun da ake yi a fannonin mu'amalar al'adu da kasuwanni, za ta yi kokarin ba da jagoranci da ingiza musanyar al'adu iri iri a tsakanin kungiyoyin jama'a da kuma hukumomi na bangarorin biyu.

(4) Hadin gwiwar kiwon lafiya

kasar Sin za ta sa kaimi a wajen yin mu'amala tsakanin likitoci na bangarorin biyu da kuma yin musanyar labaran da abin ya shafa. Kasar Sin za ta ci gaba da tura kungiyoyin ba da hidimar jiyya zuwa kasashen Afirka, kuma za ta bayar da taimakon magunguna da sauran kayayyakin jiyya gare su. Bayan haka kuma, kasar Sin za ta taimaka wa kasashen Afirka a wajen kyautata kayayyakin jiyya da horar da likitoci. Za ta kuma karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka a wajen shawo kan cututtuka masu yaduwa, ciki har da ciwon sida da malariya da dai sauran cututtuka da nazarin maganin gargajiya da yin amfani da su da kuma kafa tsarin sarrafa al'amuran gaggawa na kiwon kafiya.

(5) Yin hadin gwiwa a fannin yada labaru

A sa kaimi kan kafofin yada labaru na bangarorin nan 2 da su yi mu'amala da hadin gwiwa tsakanin rukunnoni daban daban ta hanyoyi daban daban, da kara wa juna sani, ta yadda za a ba da labaru daga dukan fannoni bisa halin da ake ciki. A kara yin cudanya da tuntuba tsakanin hukummomin da abin ya shafa na gwamnatocin bangarorin nan 2, da kuma yin mu'amalar sakamako mai kyau da aka samu wajen daidata huldar da ke tsakaninsu da takwarorinsu na gida da na waje, ta yadda za a ba da jagoranci da sauki ga kafofin yada labaru da su yi mu'amala.

(6) Yin hadin gwiwa a fannin harkokin gwamnati

A yi mu'amala da hadin gwiwa a fannonin kafa tsarin ma'aikatan gwamnati da yin kwaskwarima kan ayyukan harkokin gwamnati da kuma horar da ma'aikatan hukummomin gwamnati, a yi tattaunawa kan kafa tsarin yin hadin gwiwa da mu'amala tsakanin kasashen Sin da Afirka a fannin sha'anin ma'aikata.

(7) Yin hadin gwiwa tsakanin kananan jakadu

A yi tattaunawa ta lokaci-lokaci ko ba ta lokaci-lokaci ba tsakanin ‘yan kananan jakadu na kasashen Sin da Afirka kan al'amuran da za su warware ko kuma wadanda suke jawo hankulan bangarorin nan 2 da suka shafi huldar da ke tsakaninsu ko kuma dangantakar da ke tsakanin bangarori daban daban, don kara wa juna sani da kuma ingiza yin hadin gwiwa. A saukaka wa mutanen bangarori 2 wajen kaiwa da kawowa da kuma ba da tabbaci ga lafiyar ‘yan kaka gida na bangarorin nan 2.

(8) Cudanya tsakanin fararren hula na Sin da na kasashen Afirka

Za a karfafa zuciyar yin cudanyar da ke tsakanin kungiyoyin fararren hula na kasar Sin da na kasashen Afirka da kuma yi musu jagora, musamman ma karfafa yin cudanyar da ke tsakanin matasa da ‘yan mata domin kara fahimtar jama’ar bangarorin biyu da amincewar juna da kuma hadin gwiwa tsakaninsu. Haka kuma za a sa kaimi ga masu aikin sa kai na kasar Sin da su je kasashen Afirka domin yin aikin hidima.

(9) Hadin gwiwa kan kare muhalli

Za a karfafa yin mu’amala tsakanin Sin da Afirka kan fasahohi domin ingiza hadin gwiwarsu a fannonin canjawar yanayi da kare ruwa da hana yaduwar hamada da kuma kare halittu iri daban daban da dai sauransu.

(10) Rage bala’i da ba da taimakon agaji ga masu fama da bala’i

za a hada gwiwa tsakanin Sin da Afirka kan yin cudanya tsakanin masu aikin rage bala’i da ba da taimakon agaji ga masu fama da bala’i da horar da su da kuma fasahohin rage bala’i. Haka kuma kasar Sin za ta amsa bukatar bayar da taimakon jin kai cikin gaggawa da kasashen Afirka ke yi mata, da kuma goyon bayan kungiyar Red Cross ta kasar Sin da dai sauran kungoyoyin da ba na gwamnati ba da su yi mu’amala da hadin kai tsakaninsu da kungiyoyin da abin ya shafa na kasashen Afirka.

 
Zaman lafiya da kwanciyar hankali Kai Sama

(1) Hadin guiwar aikin soja

Kara yin ma’amala tsakanin manyan shugabannin rundunonin sojoji na bangarori biyu, da nuna himma ga yin musaye-musaye da hadin guiwa a fannin ayyukan soja na zamani. Kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako wajen horar da ma’aikatan soja domin kasashen Afrika, ta nuna goyon baya ga kasshen Afrika bisa kokarin da suke yi wajen karfafa ayyukan tsaron kasa da askarawansu don kare zaman lafiyarsu.

(2) Warware rikici da aikin kare zaman alfiya

Nuna goyon baya ga kawancen kasashen Afrika da sauran kungiyoyin shiyyoyi da kasashe da abin ya shafa bisa babban kokarin da suke yi don neman warware rikicin shiyya-shiyya, kuma ta yi abubuwa da take iya yi wajen ba su gudummowa. Yin kokarin yunkurar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ta kula da matsalolin rikici da ake samu a shiyyoyin Afrika, kuma ta ba da taimako ga daidaita su. Ci gaba da nuna wa Majalisar Dinkin Duniya goyon baya bisa aikin kare zaman lafiya da take yi a nahiyar Afrika da kuma shiga aikin nan.

(3) Hadin guiwa a fannin shari’a da harkokin ‘yan sanda

Sa kaimi ga yin musaye-musaye da hadin guiwa a tsakanin hukumomin shari’a da na aiwatar da shari’a na bangarorin biyu, su yi koyi da juna wajen kafa tsarin dokoki da yin kwaskwarima kan tsarin shari’a. Daga matsayinsu na rigakafin laifuffuka da bin bahasinsu da kuma murkushe su cikin hadin guiwa, su bai wa juna taimako wajen murkushe laifuffuka da ake yi cikin kungiya-kungiya kuma tsakanin kasa da kasa da laifuffukan cin hanci da rashawa. Su kara karfin hadin guiwarsu don bai wa juna taimako a fannin shari’a da komar da wadanda ake zarginsu da laifi gida.
Kara yin musaye-musaye da kara karfin hadin guiwa a tsakanin Sin da hukumomin kula da harkokin bakin haure na kasashen Afrika daban daban don yanke hukunci kan haramtattun bakin haure, su kara musaya wa juna labarai dangane da harkokin kula da bakin haure, su kafa kyawawan hanyoyi masu inganci da ake bi wajen bai wa juna labaru.

(4) Kwanciyar hankali da ba na musamman ba

Kara musanya rahoton leken asiri tsakanin juna, yin bincike kan hanyoyi masu inganci da ake bi wajen kara karfin hadin guiwa a fannin murkushe ta’adanci da fataucin kananan makamai da miyagun kwayoyi da barkata laifuffukan tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa da kuma sauran irinsu don kare kwanciyar hankali da ba na musamman ba, sa’an nan kuma su kara daga matsayinsu tare don magance barazana da ake sha a fannin kwanciyar hankali da ba na musamman ba.
  Babi na biyar:   Kai Sama
Taron dandalindandalin hadin kai na Sin da Afrika da kuma aikace-akace nan gaba

Taron dandalin hadin kai na Sin da Afrika da aka kafa a shekarar 2000, ya riga ya zana tsari mai amfani na Sin da Afrika da su yi tattaunawa da hadin kai na bangarori dabam daban, ya kafa muhimmin shirin kuduri, da dandamali na sabon dangantakar abokantaka ta zaman karko da dogon lokaci, da kuma ta daidaituwa da samun moriyar juna a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan taimakon da taron dandalin Sin da Afrika ya bayar wajen kara yin shawarwarin siyasa, da kuma hakikanin hadin kai da ke tsakanin Sin da Afrika, za ta yi kokari tare da kasashen Afrika a kan tabbatar da “Sanarwar Beijing ta taron dandalin hadin kan Sin da Afrika”, da “Takardar shirin hadin kai wajen tattalin arziki da bunkasuwar al'umma na Sin da Afrika”, da “Shirin ayyukan Addis Abeba na taron dandalin Sin da Afrika (2004-2006)”, da aikace-aikace nan gaba, kuma za su ci gaba da fitar da sababbin matakai a cikin shirin kudurin taron dandali, da kara amincewa da juna wajen siyasa a tsakanin Sin da Afrika, da samar da bunkasuwar hadin kai a dukan fannoni. Za su kara kyautatta tsarin taron dandali, da sa himma domin neman dabara da hanya mafi kyau a kan kara hadin kai a tsakanin taron dandali da “Shirin sabuwar hadin gwiwa don bunkasuwar Afrika”.

 
  Babi na shida:   Kai Sama
Dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kungiyoyi na shiyyar Afrika


Kasar Sin ta yabawa muhimmin taimakon da kawancen kasashen Afrika ta bayar wajen kiyaye zaman lafiya da zaman karko na shiyya-shiyya, da samar da hadin kai da bunkasuwa na Afrika, ta mai da hankali sosai kan hadin kai da kawancen kasashen Afrika a dukan fannoni, da nuna goyon baya gare ta da ta ba da amfani mai yakini a cikin harkokin shiyya shiyya da na kasashen duniya, da kuma ba da babban taimakonta ga kawancen kasashen Afrika.

Kasar Sin ta yi yabo da nuna goyon baya ga taimakon da kungiyoyin kananan shiyyoyi na Afrika suka bayar a kan samar da zaman karko na siyasa, da bunkasuwar tattalin arziki, da gudanarwar neman hadin kai a shiyyoyin kansu, kuma tana fatan kara hadin kai na abokantaka da kungiyoyi dabam daban.

 
Email Us

hausa@cri.com.cn

Contant Us Kai Sama

Tel: 8610-68892509, 8610-68892424

 
 

China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China. 100040

 
http://big5.cri.cn/gate/big5/www.beijing-olympic.org.cn/