China machoni mwetu
Mambo wanayofanya wachina katika maisha ya kila siku, yanayohusu wachina wa kawaida, na yale yanayofuatiliwa na watu wa kawaida katika jamii.
ZABI SONKA
Kamar sauran kafofin yada labarai a duniya, akwai bukatar sada zumunta tsakaninmu da masu sauraro, ko kuma tsakanin masu sauraronmu da ‘yan uwansu da abokan arziki. Don haka wannan fili yake gabatar da gaishe-gaishe, da fatan alheri wanda masu sauraronmu ke aiko mana, don mu isar masu da shi daga nan birnin Beijing na kasar Sin, tare da saka faya-faye masu dadi na Sinawa, da na Hausawa, da ma na sauran kasashe don birgewa, da nishadantar da masu saurarenmu.
SHAFA LABARI SHUNI
A wannan shiri, muna karanto littafan Hausa masu ma’ana, musamman na da can, irin wadanda aka dade da wallafa su domin su tuna mana rayuwa, da al’adunmu na Hausawa kafin zuwan Turawa da ma bayan zuwansu. A cikin littafan akwai hikimomi, da dabaru, da almara, da kuma abubuwan ban mamaki, da na ban sha’awa da birgewa, da jaruman marubutan suka yi.
AKUSHIN SINAWA
Manufar wannan shiri shi ne koya wa masu sauraronmu girke-girke na Sinawa masu sauki, wadanda kuma ake iya samun kayan hadasu a kasashen Afrika, musamman inda muke da rinjayen masu sauraronmu a harshen Hausa. Sanin kowa ne Sinawa suna da wasu dabaru masu ban sha’awa na sarrafa abinci mai dadin gaske, da suka hada da ganyaye, da kayan lambu, da kayan marmari, da ma sauran nau’o’in hatsi. Bugu da kari irin yadda aka san su da noman shinkafa kanshi, a hannu guda akwai dabarun sarrafa wannan abinci ta hanyoyi masu daman gaske.